Connect with us

Business

Farashin dala ya kai Naira dubu 1,355 a kasuwar bayan fage

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kudin Najeriya na ci gaba da shan kashi a kasuwar bayan fage, inda a yanzu ake sayar da kowacce dala akan naira 1,355 kamar yadda bincike ya tabbatar.

Advertisement

Wannan baya rasa nasaba da irin matsin tattalin arziki da halin talauci da al’ummar kasar ke ciki.

Ganduje Ya Raba Masarautun Kano Gida Biyar Ne Da Mugun nufi – Kwankwaso

Wannan kuwa na zuwa ne bayan da babban bankin Najeriya ya karbi dala biliyan biyu da miliyan 25 daga bankin saye da sayarwa na Africa da nufin farfado da dalar.

Advertisement

A watan Disamban da ya gabata zuwa farkon watan da muke ciki an sayar da dalar kan naira 1,170 zuwa 1,200 a wasu sassan kasar.

Matsin da nairar ke sha na zuwa ne dai-dai lokacin da mahukunta a kasar ke cewa sun dauki matakan da suka dace don kawo karshen matsalar.

Advertisement

A yammacin jiya zuwa dare an rika sayar da dalar akan naira 1,350 zuwa 1,355 a jihohin Abuja da Lagos.

Tashin farashin Dala a Najeriya ya zama wani abu da aka kasa gane kansa, la’akari da yadda kowanne bangaren ke ikirarin yana bada gudun mowar da ta dace, amma abun na dada hauhauwa.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending