Connect with us

News

Babbar Magana: Budurwarsa Da Saurayi Sun Sace Kayan Lefen ’Yar Uwarsa A Kano

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD BASHIR 

Kotu Ta Tsare Wata Budurwa Da Saurayinta A Gidan Yari Kan Zargin Sace Kayan Lefen ’Yar Uwarsa.

Advertisement

Kotun Musulunci ta tsare wata budurwa da saurayinta a gidan yari kan zargin sace kayan lefen ’yar uwarsa.

Rahotanni na nuni da cewa An gurfanar da saurayin da budurwarsa ne a kan zargin sata da kuma karbar kayan sata a gaban Kotun Musulunci da ke zamanta a unguwar Rijiyar Lemo a Jihar Kano.

Advertisement

Jaridun Najeriya: Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani A Safiyar Wannan Ranar Laraba

Bayan jami’i mai gabatar da kara, Usman Idris Shu’aibu Dala, ya karanto takardar tuhumar, saurayin ya amsa laifinda ake zargin sa.

Amma ita budurwar ta shaida wa alkali cewa biyu daga cikin kayan lefen da ake zargi kawai saurayin nata ya kawo mata, kuma ta mika su ga kotu.

Advertisement

Bayan sauraren su, alkalin kotun, Khadi Danbaba, ya ba da umarnin tsare su a gidan yari zuwa ranar Larabar nan.

Ya kuma ba da umarnin zuwa da iyayensu a zaman kotun da za a ci gaba ranar Laraba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending