Connect with us

News

Najeriy Na Kokarin Samun Bayanan Sirrin ‘Yan Adawa Ta Hanyar Da Bata Dace Ba  – Jami’in Binace

Published

on

1739618889092

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Wani babbban jami’in kamfanin BinanceHoldings Limited mai suna ,Tigran Gambaryan, ya zargi gwamnatin Najeriya da ƙoƙarin samun bayanan sirri na ‘yan kasar domin bibiyar ‘yan adawa da ke jam’iyyun PDP da Labour Party.

Gambaryan, wanda aka tsare na tsawon watanni takwas a Najeriya, ya bayyana hakan a shafin X ranar Juma’a, yana mai cewa gwamnatin na ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin tattalin arziki.

Advertisement

A cewarsa, an yi taro da hukumar DSS a ranar 5 ga watan Janairu, inda aka buƙaci Binance da su bi umarnin ‘yan majalisar wakilai. Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnati na ƙoƙarin yin kutse a binciken da ake yi wa Binance ta hanyar ƙirƙirar zargin cewa kamfanin ya fitar da dala biliyan 26 daga Najeriya.

Gambaryan ya ce wannan adadi ba gaskiya ba ne, domin dukkan kuɗaɗen da ake magana a kansu na cikin hada-hadar kasuwanci ne kawai a dandalin Binance.

Advertisement

Bugu da ƙari, Gambaryan ya ce wasu ‘yan majalisar wakilai uku, ciki har da Peter Akpanke da Philip Agbese, sun buƙaci a basu cin hanci na dala miliyan 150 ta hanyar kudin intanet (cryptocurrency). Ya ce sun shirya wani taro na bogi don nuna cewa binciken na gaskiya ne, alhali kuwa suna ƙoƙarin ɓoye gaskiya daga al’umma.

Har ila yau, ya zargi gwamnatin Najeriya da ƙoƙarin amfani da kamfanin Binance wajen karya dokokin sirri na ƙasa da ƙasa, domin samun bayanan masu amfani da dandalin domin bibiyar ‘yan adawa da ke zargin gwamnati da haddasa faɗuwar darajar naira.

Advertisement

A cewarsa, matsalar tattalin arziki ta samu ne sakamakon sauya manufofin kuɗi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar.

Bayan watanni da dama a tsare, a watan Oktoba 2024, gwamnatin Najeriya ta janye zargin da ake masa na wanke kuɗaɗe, bayan da gwamnatin Amurka ta sa baki a lamarin. Daga nan ne aka ba shi damar barin ƙasar.

Advertisement

Wannan lamari ya tayar da cece-kuce kan alaƙar Najeriya da Binance, da kuma yadda gwamnati ke gudanar da bincike da tsare mutane ba tare da bin ƙa’ida ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending