Connect with us

News

Durkushewar Masana’antar Yadi: Yadda Mutane 500,000 Suka Rasa Ayyukasu A Kano, Kaduna

Published

on

wuceTinubu ya bai wa Kakakin Majalisa Tajudeen lambar girma ta GCON maimakon CFR

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kakakin Majalisar Wakilai, Dr. Tajudeen Abbas, ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane sama da 500,000 suka rasa ayyukansu sakamakon durkushewar masana’antun buga yadi a jihohin Kano da Kaduna.

Advertisement

Da yake kaddamar da kwamitin Majalisa kan Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC), Abbas ya jaddada cewa masana’antar yadi, wadda ke da matukar tasiri a shekarun 1980, yanzu tana daukar kasa da mutum 20,000 saboda matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.

Najeriy Na Kokarin Samun Bayanan Sirrin ‘Yan Adawa Ta Hanyar Da Bata Dace Ba  – Jami’in Binace

Ya bayyana cewa wadannan matsaloli sun hana ci gaban yankin, tare da rage hanyoyin samun abinci ga al’umma. Duk da haka, ya yi fatan cewa NWDC za ta taka rawar gani wajen magance wadannan kalubale.

Advertisement

Kakakin Majalisar ya bukaci hukumar da ta gudanar da cikakken bincike don tantance bukatun yankin, tare da samar da shirin bunkasa yankin na tsawon shekaru 10. Ya ce shirin zai zama taswirar aiki, zai janyo masu ruwa da tsaki, kuma zai samar da hanyoyin samun kudade domin tabbatar da ingantattun ayyuka.

Ya bukaci hadin gwiwa tsakanin NWDC, gwamnatocin jihohi, sarakuna, kungiyoyin farar hula, da masu zaman kansu domin tabbatar da dorewar ayyuka. Haka nan kuma, ya nemi binciko sabbin hanyoyin samun kudade, ciki har da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, domin farfado da tattalin arzikin yankin.

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending