News
BADAƘALAR FILAYEN ₦20B A KANO: PCACC Ta Cafke Magatakardan Babban Kotu, Lauyoyi da Jami’an Tsaro
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta cafke Magatakardan Babban Kotun Kano, mataimakinsa mai ritaya, lauyoyi uku, jami’an tsaro, da wasu mutane 10 bisa zargin hannu a badaƙalar kuɗi sama da Naira biliyan 20.
Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya bayyana cewa an bankado wata ƙungiyar masu aikata laifuka da suka ƙware wajen kwace filayen jama’a ta hanyar yin jabun takardun gwamnati, samun hukunce-hukuncen kotu na bogi, da amfani da su wajen karɓe kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu.
Durkushewar Masana’antar Yadi: Yadda Mutane 500,000 Suka Rasa Ayyukasu A Kano, Kaduna
Hadin Gwiwar Lauyoyi, Ma’aikatan Kotu, da Jami’an Tsaro
Shugaban hukumar ya bayyana cewa an gano cewa wasu lauyoyi, ma’aikatan kotuna, jami’an rajistar filaye, da jami’an tsaro suna da hannu a wannan badakalar, inda suke taimakawa wajen karya doka don amfanin kansu.
“Mun gano wata ƙungiyar masu aikata laifi da ke amfani da jabun takardu da kuma hukuncin kotu na bogi domin kwace kadarorin jama’a. Abin da ya fi daure kai shi ne yadda lauyoyi da jami’an gwamnati ke taimakawa wajen aiwatar da waɗannan haramtattun ayyuka,” in ji Muhuyi Magaji.
An cafke waɗanda ake zargi bayan wata babbar kotun Kano ta bayar da umarnin kama Suleman Ali, wanda ake zargi da jagorantar badaƙalar. A cewar PCACC, daga cikin waɗanda aka kama akwai jami’ai huɗu daga ma’aikatar ƙasa da tsare-tsare, yayin da wasu suka sami beli.
Baje Kolin Shaidu da Kayayyakin da Aka Kwato
A yayin taron manema labarai, PCACC ta baje kolin wasu daga cikin shaida da aka samu, ciki har da jabun takardun tallafin filaye, rahotannin hukumar kashe gobara na bogi, da kuma makudan kuɗaɗe.
“Hatta wani jami’in DSS da ake zargi ya bayar da cin hanci da ya kai sama da Naira miliyan biyu domin a sako shi,” in ji shugaban hukumar, wanda ya yabawa jami’in da ya ƙi karɓar cin hancin.
PCACC ta kuma yabawa Babbar Kotun Kano ƙarƙashin Mai Shari’a Dije Abdu Aboki bisa goyon bayan bincike da bayar da umarnin kama waɗanda ake zargi.
“Ba Wanda Zai Tsira”
Shugaban PCACC ya jaddada cewa babu wani mutum, komai matsayinsa, da zai tsira daga hukunci idan aka same shi da hannu a cin hanci da rashawa.
“Idan da cin hanci zai iya dakatar da wannan bincike, da tuni an dakatar da shi. Amma tare da goyon bayan ɓangaren shari’a da kuma Gwamnan Jihar Kano, mun jajirce wajen ganin mun gurfanar da masu laifi a gaban kuliya,” in ji shi.
Yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da bincike, yayin da hukumar ke bankaɗo ƙarin bayanai kan yadda akeaiwatar da wannan badaƙala.
