Connect with us

News

ECOWAS Ta Sallami Ma’aikatanta 130 ‘Yan Asalin Nijar Da Mali Da Burkina Faso

Published

on

images (2)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta kawo karshen aikin ma’aikata daga kasashe uku na ƙawancen Sahel (AES) – wato Nijar, Mali, da Burkina Faso.

Advertisement

A wata sanarwa da ECOWAS ta fitar, ta bayyana cewa an miƙa wa ma’aikatan takardun sallama a hukumance, wanda ke nuna cewa ba su ƙara zama jami’an ƙungiyar ba tun bayan da kasashensu suka fice daga ECOWAS a ranar 29 ga Janairu, 2025.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kimanin ma’aikata 130 ne suka fito daga kasashen ukun.

Advertisement

BADAƘALAR FILAYEN ₦20B A KANO: PCACC Ta Cafke Magatakardan Babban Kotu, Lauyoyi da Jami’an Tsaro

Bayan ficewar su, ECOWAS ta kafa kwamiti na musamman da zai tattauna da Nijar, Mali da Burkina Faso kan tsarin ficewar su, wanda ya shafi batutuwan zirga-zirgar jama’a da kayayyaki, hanyoyin kasuwanci da tattalin arziki, da kuma kayayyakin more rayuwa da ECOWAS ta aiwatar a kasashen.

A nasa bangaren, ƙawancen AES ya bayyana cewa yana da shirin ci gaba da tattaunawa da ECOWAS, tare da tabbatar da cewa burin al’umma zai kasance a sahun gaba a duk wata yarjejeniya da za a cimma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending