Connect with us

News

MAN FETUR: Sama Da Kaso 70% Na Kuɗin Shiga Na Masu Adaidaita Sahu Na Narkewa A Sayen Mai — Rahoto

Published

on

FB IMG 1780964162210

Wani sabon bincike ya bayyana cewa hauhawar farashin man fetur na ci gaba da durƙusar da sana’ar Adaidaita Sahu a Arewacin Najeriya, inda aka gano cewa kusan kashi 73% na kuɗin da direbobin ke samu a kullum na tafiya ne kan sayen mai.

Rahoton wanda Shugaban Kamfanin Carbon Assets Limited, Mukhtar Abdulhameed, ya gabatar a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin sufuri a Arewacin ƙasar, ya bayyana yadda tsadar mai ke matuƙar rage ribar masu sana’ar, musamman a jihohin Kano, Kaduna da Jigawa.

Advertisement

Mutane 3 Sun Mutu Yayin Da Jirgin Ƙasa Ya Kife A Hanyar Warri Zuwa Itakpe

Binciken ya nuna cewa fiye da kashi 97% na masu Adaidaita Sahu sun tabbatar da cewa ribarsu ta ragu sosai tun bayan cire tallafin man fetur a Najeriya. Haka kuma, kashi 99% sun bayyana cewa tsadar mai ta jefa su cikin matsin tattalin arziƙi mai tsanani.

Advertisement

A wasu wurare, musamman a Jigawa, rahoton ya nuna cewa wasu direbobi na kashe kusan duk abin da suke samu a kullum kan mai, lamarin da ke barin sana’ar cikin yanayin da bai da tabbas.

Rahoton ya kuma nuna cewa akwai karuwar sha’awar sauya zuwa amfani da babura masu lantarki. Kashi 94 zuwa 98% na mahalarta binciken sun nuna goyon baya ga tsarin “Battery-as-a-Service (BaaS)” wanda ke ba da damar amfani da batir ta hanyar haya maimakon saye.

Advertisement

An kiyasta cewa direba na kashe kusan Naira 9,600 a kullum kan mai, amma tsarin batir zai iya rage wannan zuwa kusan Naira 4,000, wanda zai iya barin ribar sama da Naira 5,600 a rana—kimanin Naira miliyan 1.68 a shekara.

Binciken ya kuma bayyana cewa yawan amfani da Adaidaita Sahu a Kano, Kaduna da Jigawa na haifar da fitar da iskar Carbon dioxide da aka kiyasta ya kai tan 1,042,100, wanda ya yi daidai da tasirin babura kusan 190,000.

Advertisement

Rahoton ya ce idan ko kashi 10% na masu sufuri suka rungumi lantarki, hakan zai taimaka wajen rage tasirin sauyin yanayi tare da buɗe sabbin damarmakin zuba jari a fannin makamashi mai sabuntawa.

Sai dai babban ƙalubalen da aka gano shi ne rashin ingantaccen batir da dorewar amfani da shi. Kashi 77 zuwa 85% na masu sufuri sun koka kan gazawar batir a aikace, musamman a Kano.

Advertisement

Rahoton ya kuma jaddada cewa nasarar sauyin tsarin sufuri zuwa lantarki zai dogara ne da amincewar ƙungiyoyin masu sufuri, inda kashi 90 zuwa 99% na direbobi suka ce za su rungumi tsarin idan ƙungiyoyinsu suka amince da shi.

A nasa jawabin, Abosede Paul Obameso daga shirin Agile Governance and Climate Engagement ya ce:

Advertisement

“Dorewa ita ce ginshiƙi. Ba wanda ke shiga sana’a idan bai da tabbacin yadda zai ci gaba da rayuwa.”

Ya ƙara da cewa sauyin zuwa ababen hawa masu lantarki zai iya kawo sauƙi ga masu sana’a da kuma kare muhalli, amma ya kamata a tabbatar da ingantaccen tsari kafin aiwatarwa.

Advertisement

 

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending