Connect with us

News

Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Fara Kamen Baburan Adai-daita Sahu Masu Hotuna Da Rubuce-Rubucen Batsa

Published

on

images (6)

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta kaddamar da wani sabon atisayen kama baburan adai-daita sahu da ke dauke da hotunan batsa da rubuce-rubuce marasa tarbiyya a manyan titunan jihar.

Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ne ya tura jami’an sa don gudanar da wannan aiki, inda ya bayyana cewa hakan na daga cikin nauyin da ke kan hukumar na tabbatar da tsaftar hotuna da rubuce-rubuce da ke bayyana a fili ga al’umma.

Advertisement

Sanarwar ta fito ne daga Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano.

Ƙantoman Rivers Ya Buƙaci Ƙungiyar Lauyoyi Da Ta Mayar Wa Jihar Naira Miliyan 300 Da Aka Bata

“Aikinmu shi ne tabbatar da cewa babu wani hoto ko rubutu da zai cutar da tarbiyya ko dabi’un al’umma, musamman matasa, ya fito fili ba tare da tantancewa ba,” in ji Abba El-Mustapha.

Advertisement

Daraktan Sashen Dab’i na hukumar, Alhaji Abubakar Zakari Garun Babba, ya bayyana damuwa kan yadda wasu matukan babura ke lika hotuna da kalmomi da ke sabawa tarbiyyar al’umma a jikin baburansu. Ya ce wannan lamari ba za a lamunta da shi ba, kuma hukumar za ta ci gaba da gudanar da wannan aiki a fadin jihar.

A karshe, ya bukaci matukan babura da su guji aikata irin wadannan laifuka da ka iya janyo musu fushin doka, tare da yin kira ga al’umma da su bada hadin kai da goyon baya ga hukumar domin ci gaban jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending