Connect with us

News

Ƙantoman Rivers Ya Buƙaci Ƙungiyar Lauyoyi Da Ta Mayar Wa Jihar Naira Miliyan 300 Da Aka Bata

Published

on

images (2)

Wata sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnatin jihar Rivers da Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) biyo bayan janyewar NBA daga gudanar da babban taronta a jihar.

Gwamnatin Rivers ta bayar da gudummawar naira miliyan 300 domin tallafa wa taron, amma daga bisani NBA ta mayar da taron zuwa jihar Enugu, bisa dalilin dokar ta-baci da aka kafa a jihar.

Advertisement

Matashi Ya Bayyana Yadda Ya Kashe Mutane Uku Bayan Ya Kwace Wayoyi da Babura A Kano Da Jigawa

Kantoman jihar Rivers, Ibok-Ete Ibas, ya bukaci kungiyar ta mayar da kudin, yana mai cewa tun da jihar ba ta sake karbar taron ba, babu dalilin ci gaba da rike kudaden.

Sai dai a martanin da ya fito daga shugaban kwamitin shirya taron, Emeka Obegolu, kungiyar ta bayyana cewa wannan kudade ba bashin gwamnati ba ne, illa dai kyauta da gwamnati ta bayar, don haka babu dalilin mayar da su.

Advertisement

Wannan rikici na faruwa ne a daidai lokacin da NBA ke cikin sahun gaba wajen sukar dakatar da gwamnan jihar Rivers da kuma matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na kafa dokar ta-baci a jihar, wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasa da shari’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending