News
Kungiyar Eye on Kano Initiative Ta Caccaki Shugaban NBA Kan Zargin Gwamnatin Kano Ba Tare da Bincike Ba
Kungiyar Eye on Kano Initiative ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Mista Afam Osigwe (SAN), ya fitar da wata sanarwa yana sukar matakin dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a gidajen rediyo da talabijin a Kano.
A cikin wata sanarwa da Tijjani Sarki, Sakataren kungiyar, ya fitar, ya ce shugaban NBA ya yi gaggawar yanke hukunci ba tare da ya bincika gaskiyar lamarin ba.
Gwamnatin Kano Ta Kama Awaki Kan Zargin Cinye Bishiyoyi A Titunan Jihar
“Shugaban NBA ya fadi cewa gwamnatin Kano ce ta hana ’yancin faɗar albarkacin baki, amma bai nemi bayani daga gwamnatin jihar ba, balle ya samu rahoto daga reshen NBA na Kano ko ’yan jarida da ke aiki a jihar,” in ji sanarwar.
Eye on Kano Initiative ta ce ba gwamnatin Kano ba ce ta dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye, sai dai wata shawara ce da Media Executives’ Forum ta yanke a wani taro da ta yi da masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai, inda suka yanke shawarar dakatar da shirye-shiryen saboda yawan kalaman batanci da barazana da ke shiga cikin shirye-shiryen.
“Matakin an dauke shi ne don dakile kalaman da ke iya tayar da husuma, ba wai don hana mutane faɗar ra’ayinsu ba,” in ji kungiyar.
Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda shugaban NBA ya yi gaggawar cewa an take hakkin jama’a ba tare da ya bibiyi abin da ya faru ba. Ta bayyana hakan a matsayin rashin kishin kasa da rashin adalci daga shugaban babbar ƙungiyar lauyoyi a ƙasar.
Eye on Kano Initiative ta kuma kalubalanci NBA da cewa: “Ina NBA lokacin da aka kashe ’yan asalin Kano a garin Oromi na jihar Edo? Ko da ta’aziyya ne, shin an tura?”
Ta kara da cewa NBA ta yi shiru lokacin da rikice-rikicen kabilanci suka addabi Filato da kuma lokacin da aka samu hare-hare a jihohin Arewa maso Yamma kamar Kebbi, Katsina, Sokoto da Zamfara.
Ta ce haka zalika NBA ta kasa magana a kan rikicin siyasa da ya barke a Jihar Rivers da kuma wasu matsaloli da ke faruwa a Majalisar Ƙasa.
Tijjani Sarki ya ce: “Shin shugaban NBA yana zaɓen batutuwan da zai yi magana a kansu ne don kawai a jiyo sa a kafafen yada labarai, ko yana da wata ajanda ta siyasa da ta shafi Kano?”
A ƙarshe, kungiyar ta bukaci shugabancin NBA da kwamitin ladabtarwa na ƙungiyar da su ɗauki matakin ladabtar da shugaban nasu cikin awa 72, in ba haka ba za su dauki matakin shari’a don kare mutuncin jihar Kano da kafafen watsa labaran ta.