News
Gwamna Abba Ya Dakatar Da Hadiminsa Saboda Kalamai Kan Kwankwaso

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da babban mataimakin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan rahotanni daga Ma’aikatar Sufuri ta jihar, Honarabul Ibrahim Rabiu, saboda zargin yin kalamai marasa dacewa game da tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruq Ibrahim ya fitar, ta ce an dakatar da hadimin ne nan take, sannan kuma an aike masa da takardar tuhuma.
A cewar sanarwar, kalaman da Rabiu ya yi sun shafi sauya sheka da kuma wasu kalamai marasa kyau da ya danganta su da Sanata Kwankwaso, wanda gwamnatin ta ce ba su da hujja kuma sun sabawa ka’ida.
Daraktan Yada Labaran Gwamna, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce gwamnatin ta Kano ta nisanta kanta daga kalaman da Rabiu ya yi, inda ya bayyana cewa ya fadi su ne bisa ra’ayinsa na kansa.
Ya kuma ce gwamnati ta gargadi duk masu rike da mukaman siyasa da su rika kula da yaren da suke amfani da shi, tare da nisantar furucin da ka iya bata sunan gwamnati ko jagororin
jam’iyya.