News
Kwankwasiyya Ba Sa Hula Kawai Ba Ce — Taimakon Mabukata da Kyautatawa Ne, Inji Dr Auwal Nasir

Shugaban kungiyar AKM, Dr Auwal Nasir, ya bayyana cewa Kwankwasiyya ba wai sa hula ja kawai ba ce, illa wata manufa ce da ke ginuwa a kan kyakykyawar zuciya, taimakon nakasassu, da tallafa wa mabukata a kowane lokaci.
Dr Auwal ya fadi haka ne a wajen kaddamar da shirin AKY 4+4 Medical Outreach, wani shiri na jinya da aka shirya domin tallafa wa jama’a, musamman marasa galihu, da masu bukatu na musamman a fannoni daban-daban na lafiya.
Gwamna Abba Ya Dakatar Da Hadiminsa Saboda Kalamai Kan Kwankwaso
A cewarsa, “Kwankwasiyya hanya ce ta gaskiya da tausayi, wadda ke da manufar raya rayuwar talakawa ta hanyar aikin alheri da ci gaban al’umma. Wannan shiri da muke kaddamarwa wani bangare ne na irin gudunmawar da kungiyar ke bayarwa don ceto rayuka da kuma tallafa wa wadanda ke cikin bukata.”
Wannan shirin na AKY 4+4 zai shafi bayar da magunguna kyauta, duban lafiya, da shawarwari daga kwararrun likitoci, tare da samar da tallafi ga wadanda ba su da karfi su nemi magani da kansu.
An halarci taron kaddamarwar da dama daga cikin shugabannin al’umma, sun hada da shugaban karamar hukumar Nasarawa jami’an lafiya, da mambobin kungiyar Kwankwasiyya, wadanda suka yaba da wannan kokari tare da bayyana cewa hakan na kara tabbatar da cewa Kwankwasiyya na wakiltar cancanta da jinkai a aikace.