News
Hakkin Mutane Sama Da Miliyan 20 Ne A Kanka Ba Mutum Daya Kawai Ba —Kawu Sumaila Ga Gwamna Abba
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu ya ce ya kamata Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf yasa ni hakkin mutane sama da miliyan 20 ne a kanka ba mutum daya kawai ba.
Kawu Sumaila ya baiyyana hakan a wani sakon murya da Nasara Radio Nigeria ta wallafa a yau.
Ya Kamata Gwamnati Ta Gaggauta Gyaran Hanyoyin Kasarnan – Direbobin Motocin Haya
Kawu Sumaila ya kara da cewa ina bawa Gwamna Abba shawara kada ya ci amanar al’ummar Kano, amma na gamsu da matsayarsa kan ‘Tsayawa da Kafarsa’.
“Ka sani ba wai hakkin yan Kwankwasiyya kadai ne hakki ba, akwai hakkinmu da muka zo muka hadu aka kafa Gwamnati.” Inji Kawu Sumaila.
Wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Abba ya yi alƙawarin ba zai iya kallon fuskar mai gidansa ya saɓa masa ba,
Gwamnan ya fadi haka ne a wata hira da aka yi da shi ta kai-tsaye da wasu gidajen rediyo a jihar Kano a jiya Laraba da daddare.
A cewar gwamna Abba,Allah ne ya ba shi mulki, amma kuma mai gidan sa Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne sila, saboda haka ba zai biyewa duk wasu masu yunƙurin sai ya yi masa butulci ba.
Ya ce sun shafe kusan shekaru 40 da Kwankwaso, saboda haka bai ga amfanin yin rigimar da shi ba a yanzu bayan tun a da bai yi fada da shi (Kwankwaso) ba.
“Ni a gani na cin fuska ne ka ce min wai na tsaya da ƙafa ta. Ni fa Allah ne ya bani wannan mulki, amma Kwankwaso ne sila.
“Wanda ya yi min wannan shi ne ake so in fito in yi masa butulci in yi fada da shi, to karyar ku ta sha ƙarya.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
