News
Ya Kamata Gwamnati Ta Gaggauta Gyaran Hanyoyin Kasarnan – Direbobin Motocin Haya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Direbobin motocin haya dake jihohin Kaduna, Kano da Katsina sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran hanyoyin dake jihohin domin rage wa direbobin wahalolin da suke fama da su a hanyoyin.
Matuka motocin sun yi wannan kira ne a hirar da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.
Direbobin sun ce rashin kyan hanyar a jihohin na kawo haddura da dama wanda ke sanadiyyar rayukan da dukiyoyin mutane, yi wa mutane fashi, dadewa a tafiya sannan da yawan zuwa wajen kanikawa domin gyaran motocinsu.
Bayan haka wani kwararre a harkokin tsare-tsaren birane Francis Bisallah ya ce rashin amfani da kayan aiki masu Inganci da wasu yan kwangila masu gyaran hanya ke yi na daga cikin matsalolin dake lalata hanyoyin a kasar nan.
“Rashin amfani da kayan aiki masu Inganci ya sa da zaran an kammala gina ko gyaran hanya za ka ga hanyoyin sun fara Lalacewa.
Bisallah ya yi kira ga gwamnati da ta tsaro hanyoyin sa ido domin tabbatar da kamfanonin da aka basu kwangilar gyaran hanya ko gina hanya sun yi amfani da kayan da suka dace.
Shugaban Hukumar Kula da Hanyoyi na jihar Katsina KASSAROTA Yahaya Garba-Rimi ya yi kira ga mutane da su kiyaye sharuddan hanyar da hukumar ta bada.
Garba-Rimi ya ce sharuddan sun hada da a daina zuba shara akan hanyar domin yin haka baya gyara illar ya kara lalata hanyar, masu siyar da kaya a hanya musamman wadanda ke kasa kayan su a hanyoyin da aka yi domin mutane su rika bi su daina yin haka sannan a daina wanke motoci ko babura a bakin hanya.
Bayan haka wani lauya a jihar Kano Isaac Aliyu ya ce rashin ware wa hanyoyi kudade musamman a kasafin kudaden shekara, cin hanci da rashawa da rashin gyara hanyoyi lokaci-lokaci na daga cikin matsalolin da ya sa ake fama da rashin kayan hanyaa kasar nan.
Aliyu ya yi kira ga gwamnati da ta ware isassun kudade domin ginawa da gyaran hanyoyin a kasar nan.
Wani dan kungiyar Kare Rajin Dan Adam dake Kano Bala Burakita ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta raba haƙƙin ginawa da gyaran hanyoyin da sauran sassan gwamnati cewa yin haka zai taimaka wajen ganin an gyara hanyoyin kasar nan a lokutan da ya kamata.
