News
Matashi Ya Bayyana Yadda Ya Kashe Mutane Uku Bayan Ya Kwace Wayoyi da Babura A Kano Da Jigawa
Wani matashi mai suna Umar Auwal, wanda aka fi sani da Abba Dujal, dan asalin karamar hukumar Wudil a jihar Kano, ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano tare da amsa cewa shi ne ya aikata kisan mutane uku da fashi a jihohin Kano da Jigawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matashin ya bayyana cewa ya dade yana aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da makami, satar babura da kuma kwacen wayoyi a sassa daban-daban na Kano da Jigawa.
Jam’iyyar NNPP Ta Mutu Murus Domin Kwankwaso Na Shirin Dawowa APC – Ganduje
A cewar SP Kiyawa, Abba Dujal ya bayyana cewa a unguwar Sabon Gari da ke Kano, ya kashe wani mutum sannan ya kwace masa waya kirar Infinix Hot 40i, wadda daga bisani ya sayar da ita kan naira 40,000. A wani wuri daban, ya kara kashe wani mutum tare da kwace masa waya kirar Samsung S26, wadda ya sayar da ita akan naira 160,000.
Haka zalika, ya bayyana cewa a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ya kashe wani mutum domin ya sace masa mashin.
Rundunar ‘yan sanda ta ce an fara cikakken bincike kan lamarin, kuma ana shirin gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.
Ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da ba da hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen kama masu aikata laifuka, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma.
