Connect with us

News

Fursunoni 3 Sun Yi Nasarar lashe Gasar Al-Ƙur’ani Mai Girma Ta Kano

Published

on

IMG 20250214 WA0333

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, ta shirya gasar musabaƙar Al-Qur’ani mai girma ga wasu daga cikin fursunoninta, inda uku daga cikinsu suka yi nasara.

Advertisement

Mai magana da yawun hukumar, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya bayyana cewa an shirya gasar ne domin kyautata halayyar masu zaman gidan yari tare da nufin sauya tunaninsu, domin su zama mutane masu amfani ga al’umma bayan sun kammala wa’adinsu.

ECOWAS Ta Sallami Ma’aikatanta 130 ‘Yan Asalin Nijar Da Mali Da Burkina Faso

Fursunan da ya lashe gasar yana tsare a Gidan Yarin Kumawa, inda ya samu kyautar Naira dubu dari (₦100,000). Na biyu yana tsare a Gidan Yarin Goron Dutse, ya kuma samu kyautar Naira dubu 50 (₦50,000), yayin da na uku da ke Gidan Yarin Janguza ya karɓi Naira dubu 20 (₦20,000) .

Advertisement

A yayin taron karramawar, Shugaban Kungiyar Alarammomi, Gwani Shuaibu Shehu, ya yaba wa Kwamturolan Hukumar Gidajen Yari ta Jihar Kano bisa shirya gasar, wanda ya ce hakan zai taimaka wajen cusa dabi’u masu kyau a zukatan fursunoni.

Har ila yau, ya jinjinawa Ko’odinetan hukumar kan harkokin addini, DSC Murtala Nasidi Kabara, bisa jajircewarsa wajen koyar da fursunoni karatun Al-Qur’ani.

Advertisement

A nasa jawabin, Kwanturolan Hukumar Gidajen Yari na Kano, Ado Inuwa, ya nuna godiyarsa ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, bisa halartar gasar da kansa, wanda hakan ya ƙara wa taron daraja.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending