Connect with us

News

Abubakar Sabo Ya Karɓi Rantsuwar Kama Aiki A Matsayin Sabon Shugaban Ƙungiyar Daliban Hausa Na AKCOE Da FUDMA

Published

on

IMG 20250215 WA0015

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Sabon zababben shugaban kungiyar daliban Hausa na Kwalejin Ilmi ta Aminu Kano (AKCOE) tare da hadin gwiwar Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), Kwamared Abubakar Sabo, ya bayyana kudurinsa na hada kai da duk masu kishin bunkasa harshen Hausa a ko’ina suke domin cigaban al’umma.

Advertisement

Kwamared Sabo ya bayyana hakan ne jim kadan bayan an rantsar da shi tare da sauran sabbin shugabannin kungiyar a bikin da aka gudanar.

ECOWAS Ta Sallami Ma’aikatanta 130 ‘Yan Asalin Nijar Da Mali Da Burkina Faso

A yayin taron, Shugaban Kwalejin, Dakta Ayuba Ahmad, wanda Daraktan shirye-shiryen makarantar, Dakta Dalladi Abdu, ya wakilta, ya bukaci sabbin shugabannin da su kasance jakadu nagari a duk inda suka tsinci kansu.

Advertisement

Haka nan, a jawabansu daban-daban, Dakta Ibrahim Muhammad, Daraktan kula da harkokin dalibai (Dean Students Affairs), da Shugaban Sashen Hausa, Dakta Mahe Isah Ahmad, sun yi kira ga shugabannin da su zama masu hakuri, juriya, gaskiya da amana a gudanar da ayyukansu.

Taron dai ya samu halartar jama’a da dama, ciki har da Sakataren Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Kano, Kwamared Abubakar Shehu Kwaru, da Shugaban Kungiyar Daliban Makarantar, Kwamared Najib Kabir.

Advertisement

Daga cikin sabbin shugabannin da aka rantsar akwai Rabi Ahmad Abubakar a matsayin Mataimakiyar Shugaba, Murja Murtala Mukhtar a matsayin Ma’aji, da sauransu.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending