News
Kotu Ta Aike Da Masu Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Zuwa Gidan Yarin Kuje
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta aike da wasu daga cikin waɗanda suka gudanar da zanga-zangar tsananin rayuwa zuwa gidan yarin Kuje, bayan sun ƙi amda tuhumar laifin cin amanar ƙasa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa mai shari’a Emeka Nwite ce ta bayar da umarnin a ajiye su har zuwa lokacin da za a saurari shari’a dangane da bayar da belinsu ranar 11 ga watan Satumba.
Manya-Manyan ‘Yan Adawa A Najeriya Na Tattaunawa Kan Hadaka Gabanin Zaben Shekarar 2027
Mutanen da ake tuhumar dai sun musanta dukkan laifukan da gwamnatin tarayyar Najeriya ke tuhumar su da aikatawa guda shida da suka jiɓanci ta’addanci.
Advertisements
