News
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Samu Yabo Kan Gyara Da Inganta Asibitoci A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa gyara da inganta asibitoci a fadin jihar.
Dr. Labaran ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da shugaban sashen hulɗa da jama’a na ma’aikatar lafiya, Ibrahim Abdullahi, wanda kuma ya rabawa kafafen yaɗa labarai.
Ma’aikatar Gine-gine Ta Najeriya NIOB Ta Karrama Ma’aji Sumaila da Lambar Girmamawa
A cewarsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawuran inganta kiwon lafiya tun lokacin kamfen dinsa, ciki har da samar da asibitin gaba ɗaya a kowace ƙaramar hukuma da ba ta da shi da kuma samar da cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko a kowane gunduma a cikin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.
Saboda haka, kwamishinan ya bayyana cewa wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ana inganta su zuwa matakin manyan asibitoci domin cika wannan alkawari, tare da sauƙaƙa wa al’umma samun lafiya cikin sauƙi.
Ya ƙara da cewa abin takaici ne ace wani mutum daga wata ƙaramar hukuma mai nisan sama da kilomita 100 ya riƙa wahalar tafiya domin neman magani a wani wuri, don haka burin gwamnatin jihar shi ne kowace ƙaramar hukuma ta mallaki asibitin gaba ɗaya tare da kwararrun ma’aikata da za su kula da lafiyar jama’a.
Dr. Labaran ya yi kira ga jama’a da su mara wa gwamnati baya wajen gyara da inganta sashen lafiya tare da tabbatar da cewa an kula da kayayyakin aikin asibitoci don guje wa barnata su ko satar su da wasu miyagu ke yi.
Haka kuma, kwamishinan ya tunatar da jama’a cewa likitoci da sauran ma’aikatan lafiya mutane ne kamar kowa, suna iya yin kuskure ba da gangan ba yayin gudanar da ayyukansu, don haka ya dace a ba su dama su aiwatar da aikinsu bisa ƙa’idojin da suka shafi sana’arsu.
A gefe guda, ya gargadi ma’aikatan lafiya da su guji cin zarafin marasa lafiya da ke zuwa neman kulawa, yana mai jaddada cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta amince da irinwannan hali ba.
