News
Yamutsi A Filin Idi: Mutane Biyu Sun Mutu, 20 Sun Jikkata A Gombe
An samu tarzoma a filin idi na Gombe a yayin bukukuwan Sallah, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata 20. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:45 na safe, jim kadan bayan an kammala sallar Eid da Limamin Gombe ya jagoranta, tare da halartar Gwamna Inuwa Yahaya da Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa yamutsin ya faru ne a lokacin da jama’a ke kokarin ficewa daga filin idi, lamarin da ya haddasa turereniya, musamman a bakin kofar fita. Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane 22 ne lamarin ya shafa, ciki har da yara biyu da suka rasu, Aisha Salisu Ahmed mai shekara hudu da rabi, da Maryam Abdullahi Gwani mai shekara huɗu.
Gwamnan Edo Ya Tuɓe Kwamandan Rundunar Tsaro Da Rusa Ƙungiyoyin Bijilante A Fadin Jihar
Kakakin ‘yan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa tarzomar ta samo asali ne daga cunkoson jama’a da zafi mai tsanani. Ya kara da cewa an gaggauta kai wadanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban domin kulawa da lafiyarsu.
Hukumar ‘yan sanda ta bayar da shawarar buɗe dukkan kofofin shiga da fita a irin waɗannan taruka don hana aukuwar irin wannan iftila’i anan gaba.
