Connect with us

News

Gwamnan Edo Ya Tuɓe Kwamandan Rundunar Tsaro Da Rusa Ƙungiyoyin Bijilante A Fadin Jihar

Published

on

images

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya sanar da dakatar da dukkan kungiyoyin ƴan bijilante a fadin jihar, tare da cire Kwamandan jami’an tsaro na jihar, CP Friday Ibadin (mai ritaya).

Wannan mataki ya biyo bayan kisan wasu matafiya 16 ƴan Arewa da aka yi a garin Uromi na Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa a ranar 27 ga watan Maris. A cewar wata sanarwa daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Musa Ikhilor, an bayyana cewa waɗanda suka aikata kisan ba su da rajista da hukumar tsaro ta jihar.

Advertisement

Yan Sandan Kano Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kai Wa Sarkin Kano Hari, Da Kisan Ɗan Bijilanti

Gwamnan ya tabbatar da cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kamo ragowar masu hannu a lamarin.

Ya kuma jaddada cewa dokar ƙasa ta ba kowane ɗan ƙasa ‘yancin yin zirga-zirga da gudanar da sana’arsa ba tare da wani cin zarafi ko muzgunawa ba. Gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da gwamnatin Jihar Kano, kasancewar galibin waɗanda aka kashe ƴan asalin Kano ne.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending