News
Zazzabin Lassa: Cutar Ta Yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku – Hukumar NCDC
Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa cutar zazzabin Lassa ta yi ajalin mutum 118 a fadin kasar nan cikin watanni uku kacal.
Sani Datti, jami’in yada labarai na hukumar, ya sanar da hakan a ranar Lahadi, yana mai cewa an samu mutum 3,465 da ake zargin sun kamu da cutar lassa daga watan Janairu zuwa Maris, a kananan hukumomi 91 dake jihohi 33.
YANZU-YANZU: Gwamna Edo Ya Ziyarci Kano, Ya Ba da Tabbacin Adalci Kan Kisan Mafarauta 16
A cewarsa, an tabbatar da mutum 645 sun kamu da cutar bayan gwajin jini, ciki har da jami’an lafiya 20. Jihar Ondo ce ta fi yawan jami’an lafiya da suka kamu da cutar (8), sai Bauchi (4), Edo (1), Taraba (1), Ebonyi (1), Gombe (1), Benuwe (1), da Ogun (1).
Datti ya bayyana cewa gwamnati ta aika da jami’an lafiya don gudanar da bincike da wayar da kai a jihohi 10 da suka hada da Kogi, Filato, Ondo, Edo, Bauchi, Ebonyi, Taraba, Benue, Gombe, da Nasarawa.
Shugaban NCDC, Jide Idris, ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da masu zaman kansu da su goyi bayan yaki da cutar ta hanyar samar da magunguna da fadakar da jama’a. Haka kuma, ya bukaci jami’an lafiya su kara kokari wajen gano cutar da kula da masu fama da ita.
Ya kuma shawarci ‘yan kasa da su tsaftace muhallansu, jikinsu, da abincinsu domin gujewa kamuwa da cuta.
