Connect with us

News

An Kama Wasu Jami’an Tsaro Huɗu Da Ake Zargi Da Taimakawa Ayyukan Ta’addanci

Published

on

FB IMG 1746314435431

Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta tabbatar da kama wasu jami’an tsaro huɗu da ake zargi da taimakawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Bisa bayanan da Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ya fitar, an cafke jami’an ne a yayin wani samame da dakarun tsaro suka gudanar daga ranar 26 zuwa 29 ga Afrilu, 2025 a ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali dake Jihohin Borno da Adamawa.

Advertisement

Kotu Ta Tura Amarya Da Angonta Gidan Yari A Kano 

Manjo Janar Kangye ya bayyana cewa, biyu daga cikin jami’an da aka kama na daga cikin rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojojin ƙasar wajen yaƙi da ta’addanci.

“A cikin waɗanda muka kama akwai jami’an tsaro da ke bai wa ’yan ta’adda bayanai da kayan aiki. Wannan lamari abin takaici ne kuma ya nuna irin cin amanar da ke faruwa a cikin rundunar,” in ji Kangye.

Advertisement

Ya ƙara da cewa, rundunar sojoji ta kama wasu ’yan ta’adda huɗu da ke da alaƙa da waɗannan jami’ai, kuma an tabbatar da cewa suna taimaka wa masu kai farmaki da kayayyakin yaƙi da bayanan sirri.

Manjo Janar Kangye ya yi kira ga kwamandojin runduna da su ƙara sa ido tare da wayar da kan jami’ansu dangane da illar haɗa kai da ’yan ta’adda, yana mai cewa irin wannan cin amanar na iya hana nasarar da ake kokarin samu a yaƙin da ake yi da ta’addanci.

Advertisement

A wani farmaki na daban, rundunar sojoji da dakarun haɗin gwiwa sun kai hare-hare masu haɗa da sintiri na yaƙi, samame, da aikin share fage a ƙananan hukumomin Gwoza, Dikwa, Bama, Chibok, Gujba, Geidam da Yunusari.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending