News
Doka Ba Ta Bai Wa Jami’an Tsaro Ikon Kama ’Yan Uwan Masu Laifi Ba, Idan Ba A Kama Wanda Ake Zargi Ba — Lauya
Doka Ba Ta Bai Wa Jami’an Tsaro Ikon Kama ’Yan Uwan Masu Laifi Ba, Idan Ba A Kama Wanda Ake Zargi Ba — Lauya
Wata lauya a Jihar Kano, Barista Asiya Muhammad Imam, ta ce dokar ƙasa ba ta bai wa jami’an tsaro damar kama ko tsare ’yan uwan mutum idan ba a samu wanda ake zargi da aikata laifi ba.
Barista Asiya, wadda ke aiki a ofishin lauyoyin gwamnatin Jihar Kano da ke Gidan Murtala, ta bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan al’umma da Cibiyar Isa Wali ta shirya a unguwar Rimin Keɓe, ƙaramar hukumar Ungogo.
Taron ya mayar da hankali ne kan tanade-tanaden Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta Jihar Kano (ACJL) ta 2019, a ƙarƙashin shirin samar da adalci ga kowa, Justice for All (II).
A cewar lauyar, kama mutum saboda laifin da bai aikata ba, musamman kasancewarsa ɗan uwan wanda ake nema, ya saɓa wa ka’idar adalci da kuma haƙƙin ɗan Adam da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Ta jaddada cewa wajibi ne jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu bisa doka, tare da mutunta haƙƙin ’yan ƙasa a dukkan matakan bincike da kama mutane.
Taron, wanda ya haɗa mata da masu nakasa, ya kuma yi kira ga iyaye mata da su daina ɓoye laifukan ’ya’yansu idan suka aikata, domin hakan na taimakawa wajen inganta tarbiyya da rage aikata laifuka a cikin al’umma.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
