Connect with us

News

An kama yan Najeriya 109 kan zargin safarar kwayoyi a Indiya

Published

on

Copy of Copy of Copy of Copy of Copy of Copy of Copy of Queen Of All Mayhem 54

Ƴansanda a jihar Maharashtra na Indiya sun ce sun tsare wasu ƴan Najeriya 109, waɗanda suka kama kan laifin zama ba bisa ka’ida ba a ƙasar, inda suka ce sun ƙwace hodar iblis mai nauyin kilogram biyu a wajen miutanen.

Hukumomin ƙasar sun ce babu wanda yake da cikakkun takardun zama cikin mutanen, waɗanda ke zaune a birnin Nalasopara da ke gabashin ƙasar.

Advertisement

Gamayyar ’Yan Kasuwar Man Fetur Ta Bukaci FCCPC Ta Binciki Zargin Da Akewa Matatar Dangote Na Mamaye Dukkan Damarmaki

An kai samame yankin ne da misalin karfe 6 na safe, a cewar mataimakiyar kwamishinan ƴansandan yankin Poornima Chowgule-Shringi.

“A lokacin samamen ne muka samu damar ƙwace hodar iblis mai nauyin giram 2 daga hannun wani mutum,” in ji ta.

Advertisement

An sha samun hannun ƴan ƙasashen waje daga Najeriya, Uganda da kuma Ghana waɗanda ke rayuwa a Nalasopara da Achole da kuma Tulinj a batun safarar miyagun ƙwayoyi, in ji jami’ar ƴansandan.

 

Advertisement

 

FREE PRESS JOUNAL

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending