Connect with us

News

Yarjejeniyar Kasar Rasha Da Amurka Kan Makamin Nukiliya Ta Kawo Karshe

Published

on

images (5)

Yarjejeniyar makamin nukiliya tsakanin kasar  Amurka da Rasha na ƙarewa a yau Alhamis, abin da ke nuna da cewar a karan farko cikin shekaru 50 dukkanin ƙasashen ba su da wani waigi wurin ƙara adadin makamin nukiliya da suke da shi

Ƙarewar wannan yarjejeniyar nukuliya tsakanin manyan ƙasashen duniyar wato Amurka da Rasha zai kafa ɗambar wata sabuwar fargaba kan yadda ƙasashen ke da ikon yin rige-rigen mallakar bunƙasa makamansu na Nukiliya.

Advertisement

Doka Ba Ta Bai Wa Jami’an Tsaro Ikon Kama ’Yan Uwan Masu Laifi Ba, Idan Ba A Kama Wanda Ake Zargi Ba — Lauya

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce a shirye yake ya ci gaba da aiki da wannan yarjejeniya zuwa nan da shekara guda, muddin Washington ta bi sahunsa wurin yin haka, to amma shugaban Donald Trump bai nuna sha’awar tsawaita yarjejeniyar ba.

Advertisement

Trump ya sha nanata alamun ƙayyade mallakar makaman nukiliya kuma zai sanya China cikin tattaunawa kan batun.

Mai bai wa Putn shawara Yuri Ushakov ya ce shugaban Rasha ya tattauna ƙarewar yarjejeniyar da shugavan China Xi Jinping amma ya ce Washignton ba ta ce uffan ba kan buƙatar tsawaita yarjejeniyar.

Advertisement

Masu rajin tabbatar da taƙaita ƙaruwar makamai sun sha nuna damuwa an ƙarewar wannan yarjejeniya, tare da gargaɗin cewa ƙarewarta zai buɗe wani fagen rige-rige kan bunƙasa makamin niukiliya tsakanin ƙasashen lamarin da zai iza rashin ytabbas da ta’azzara barazanar amfani da makamin nukiliya.

A gefe guda shima babban limamin ɗarikar Katolika Fafaroma Leo a ranar Laraba ya yi kira da cewa kada a yi watsi da wannan yarjejeniya tare da buƙatar ganin ta ci gaba da aiki.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending