News
“Ya Kamata Gwamnatin Kano Ta Gaggauta Dakile Sabuwar Ɗabi’ar Rike Hannu Tsakanin Samari da ’Yan Mata” — Dr Abubakar Tijjani
Wani malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (Kano State Polytechnic), Dr Abubakar Tijjani Ibrahim, ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta gaggauta daukar mataki kan sabuwar ɗabi’ar da ke yaduwa tsakanin samari da ’yan mata na rike hannun juna da sunan soyayya a lokacin bukukuwa da shagulgula.
Malamin ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa Facebook, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda wannan ɗabi’a ke kara yaduwa musamman a shagulgulan biki da wasannin nishadi.
“Yanzu haka samari da ’yan mata suna taruwa a waje guda, suna jerin layi, kowanne yana fitowa yana kama hannun wanda ya zaɓa. Wannan ba al’ada ba ce, kuma ba dabi’ar addini ba ce,” in ji shi.
Ya ce irin wannan halayya tana ci gaba da bazuwa a kafafen sada zumunta, kuma har wasu jihohin Arewa sun fara kwaikwayonta, lamarin da ya ce yana kara dagula tarbiyyar matasa.
“A yayin da muke ta kokarin yaki da wasu halayen banza da ke lalata tarbiyya, sai gashi an fito da wata sabuwa da ta fi muni. Wannan ya nuna akwai matsala babba a cikin al’umma,” in ji Dr Abubakar.
Malamin ya ce hakan ya sabawa koyarwar addini da al’adun Hausawa, kuma idan aka ci gaba da yi shiru, za ta kara dagula al’amura.
Don haka ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano da kuma Hukumar Hisba da su dauki matakin gaggawa domin dakile yaduwar wannan dabi’a da ya kira “ta’asa”.
