News
An kama ‘yan fashi 6 A Kano
Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Kano ta samu gagarumar nasara a yaki da masu aikata laifuka, inda ta cafke wasu mutum shida da ake zargi da hannu a satar motoci a Kano da wasu jihohin makwabta.
A cewar Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, an kama wadanda ake zargi ne a cikin jerin samame daban-daban da aka gudanar bisa umarnin Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.
SP Kiyawa ya bayyana cewa, a ranar 10 ga Mayu, 2025, CSP Rabiu Gidado ya jagoranci wani samame a Jihar Filato, wanda ya kai ga kama Saidu Abubakar da wata mota kirar Toyota Corolla da aka sace daga yankin Na’ibawa da ke Kano.
Haka kuma, a wani samame da aka gudanar a ranar 1 ga Mayu, an kama wasu mutum uku: Abdulaziz Usman, Umar Abubakar, da Sunusi Abdullahi, bayan da suka kai hari wani gida a Hotoro da safiyar ranar, inda suka sace mota kirar Toyota Yaris, kwamfutoci uku, waya kirar iPhone 11, da kudi har naira dubu dari da biyu (₦200,000). Bincike ya kai ga kama wani mai siyan kayan sata daga Kaduna da kuma kwato wasu motoci guda biyu.
Bugu da ƙari, a ranar 16 ga Mayu, an kama Ibrahim Isa a Jihar Filato yayin da yake ƙoƙarin sayar da wata motar siminti (concrete mixer) da aka sace daga Jihar Jigawa.
SP Kiyawa ya bayyana cewa, dukkanin waɗanda ake zargi suna hannun ‘yan sanda, kuma suna bayar da haɗin kai a binciken da ake gudanarwa kafin a gurfanar da su a gaban kotu.
A nasa bangaren, Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jajircewar jami’ansa, tare da tabbatar wa da al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya kuma bukaci hadin kan al’umma wajen bayar da sahihan bayanai domin tunkarar miyagun laifuka.
