News
Magidanci Ya Cinna Wa Matarsa Da Ƴaƴansa Wuta
An shiga firgici da tashin hankali a ƙauyen Onicha Ngwa da ke cikin karamar hukumar Obingwa a jihar Abia, bayan da wani magidanci ya cinna wa kansa da matarsa da ƴaƴansa uku wuta, bisa zargin cin amana a aurensu.
Rahotanni sun bayyana cewa magidanci mai suna Udochi Amala, ɗan shekara 40, ya aiwatar da wannan mummunan aiki ne bayan samun sabani da matarsa Amarachi, inda ya zarge ta da cin amana. Bayan ya cinna wuta, ya ƙoƙarta guduwa, amma jami’an tsaro sun kama shi.
Saudiyya Ta Kama Matar Da Mahaifiyar Fitaccen ’Dan Bindiga Ado Aliero
Wata daga cikin ƴaƴan su ta rasu sakamakon ƙonewar da ta yi, yayin da ake zargin cewa matar da sauran ƴaƴan biyu suma sun mutu, in ji rahotanni na farko.
Da yake karin bayani, Udochi ya ce: “Ina da matsala da matata, amma ban yi tsammanin za ta kai wannan matakin ba. Na gaji da rayuwa ne kawai. Ban taɓa kama ta da wani ba, sai dai ina zarginta.”
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Abia, ta bakin mai magana da yawunta DSP Maureen Chinaka, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakkun bayanai.
Ƙungiyar lauyoyi mata ta duniya (FIDA) reshen jihar Abia ta bayyana matuƙar damuwa da ɓacin rai kan wannan lamarin, tana mai cewa hakan babban laifi ne da ya sabawa ɗabi’a da mutuncin ɗan adam. Kungiyar ta bukaci hukuma ta tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
FIDA ta kuma yi kira da a ƙara wayar da kan al’umma game da muhimmancin sasanci da neman mafita ta hanyar doka a duk lokacin da rikici ya taso a cikin gida, maimakon aikata kisan gilla ko daukar doka a hannu.
