News
Ma’aikatan KEDCO Za Su Tsunduma Yajin Aiki
Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) za su shiga yajin aiki daga daren Talata, bisa zargin gazawar kamfanin wajen biyan kudaden fansho na ma’aikata.
Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa (NUEE) reshen shiyyar Kano — wadda ta kunshi jihohin Kano, Jigawa da Katsina — ce ta sanar da hakan a daren Talata.
Babban Sakataren Tsare-Tsaren kungiyar, Comrade Muhammad Babangida Muhammad, ya shaida wa Arewa Updates cewa yajin aikin zai fara ne daga karfe 12 na dare.
Ya ce sun dauki matakin ne bayan dogon jinkiri da suka ce KEDCO ta yi wajen biyan hakkokin fanshon ma’aikatan da suka yi ritaya.
“Mun gaji da jira da kuma alkawuran da ba a cika ba. Don haka yajin aikin nan ba zai tsaya ba sai an biya bukatun ma’aikata,” in ji shi.
Yanzu haka, ana sa ran yajin aikin zai shafi samar da wutar lantarki a wasu sassan jihohin da KEDCO ke kula da su.
