Connect with us

Politics

Jam’iyyar PDP Ta Roƙi Peter Obi Ya Koma Cikinta

Published

on

Spread the love

Jam’iyyar PDP reshen jihar Anambra ta roƙi tsohon gwamnan jihar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, da ya dawo jam’iyyar domin ƙarfafa ta a fagen siyasa.

Wannan na cikin abubuwan da suka fito daga wani babban taron kwamitin zartarwar jam’iyyar na jihar da aka gudanar a Awka, babban birnin jihar, a ranar Alhamis.

‎‎Za’a Fara Shigar Da Kararraki Ta Hanyar Amfani Da Internet A Manyan Kotunan Tarayya 

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Ndubisi Nwobu, ya ce Peter Obi yana da muhimmiyar rawa da zai taka wajen ceto jam’iyyar daga halin da take ciki a yanzu.

Advertisement

Ya ce, “Obi ya taka muhimmiyar rawa a tarihin jam’iyyar PDP a jihar Anambra. Dawowarsa zai taimaka wajen farfaɗo da jam’iyyar da kuma haɗa kan ’ya’yanta da suka watse.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyar na shirin kafa wani kwamiti da zai tuntubi tsoffin ’ya’yan jam’iyyar da suka fice, ciki har da Peter Obi, domin tattaunawa da su kan yiwuwar dawowa.

Peter Obi ya taba zama gwamnan jihar Anambra karkashin jam’iyyar APGA, kafin daga bisani ya koma PDP inda ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Atiku Abubakar a 2019. Daga bisani ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar Labour kafin zaɓen 2023 da ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Advertisement

A lokacin zaɓen 2023, Peter Obi ya samu gagarumar nasara a jihar Anambra da sauran sassan Kudu maso Gabas, lamarin da ya nuna irin karɓuwa da goyon bayan da yake da shi a yankin.

 

 

Advertisement

DAILY POST 

 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *