News
Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Taron Ƙasa Don Inganta Ƙirƙira Da Tattalin Arzikin Najeriya
Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki sabon mataki na ƙarfafa ci gaban tattalin arziki ta hanyar ƙaddamar da kwamitin shirya babban taron ƙasa kan harkar ƙirƙira, wanda ake sa ran zai zama dandalin musayar ra’ayi da gina haɗin gwiwa tsakanin masana da masu ruwa da tsaki a fannin kirkire-kirkire da fasaha.
An kaddamar da kwamitin ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda ya bayyana cewa wannan shiri wata dama ce ta haskaka irin basira, fasaha da damar kirkira da Kano ke da ita, musamman a fannin al’adu da kayayyakin gargajiya.
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 1,111, Sun Yi Garkuwa Da 276 A Cikin Wata Ɗaya — Rahoto
Kwamared Waiya ya ce: “Wannan taro zai fito da irin hikima da basirar da ke cikin al’ummar mu, kuma zai jawo hankalin duniya kan irin gudunmuwar da wannan fanni zai iya bayarwa ga cigaban tattalin arzikin Najeriya.”
Ya jinjina wa Gidauniyar Kannywood bisa shiryawa da fitowa da wannan tunani mai ma’ana, yana mai cewa hakan ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na amfani da kirkira da al’adu wajen haɓaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Haka zalika, ya nuna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bayarwa a kowane mataki, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da ke ganin muhimmancin kirkira a tsarin ci gaban al’umma.
Kwamitin da Kwamared Waiya ke jagoranta ya kunshi kwamishinoni, masana, da wakilan ƙungiyoyi daga fannoni daban-daban – ciki har da fina-finai, kayan ado, adabi da sauransu – wadanda za su shirya taron da ake sa ran zai samar da sabbin hanyoyin dogaro da kai ga matasa da masu fasaha.
Taron dai, idan ya kammala, zai ƙarfafa gwiwar masu kirkira, da buɗe damammakin kasuwanci, da kuma samar da sabbin hanyoyin samar da ayyukan yi ga al’umma a jihar da ƙasa baki ɗaya.
