Connect with us

News

‎Jami’an Tsaro Sun Cafke Mutum Bisa Mutuwar Yaro Ɗan Shekara Uku A Ramin Kwatar Gidansa

Published

on

download (1)

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mazaunin unguwar Durumi-2, Philip Jallo, bisa zargin sakaci da ya haifar da mutuwar wani yaro ɗan shekara uku da ya faɗa cikin wani ramin kwata a harabar gidansa.

‎Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, inda ta ce lamarin mai tayar da hankali ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare, a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2025.

‎Yadda Rashin Ruwa Ya Ke Hana Yara Mata Damar Zuwa Makaranta A Shanono ‎

‎A cewar sanarwar, yaron marigayi ya faɗa cikin wani rami da ke cike da najasa wanda aka ce ya dade a buɗe ba tare da an rufe shi ba, duk kuwa da koke-koken da mazauna yankin ke ci gaba da yi kan hatsarin da ramin ke haifarwa.

‎“Bincikenmu ya tabbatar da cewa mazauna yankin sun sha roƙon wanda ake zargi da ya dauki matakin rufe ramin, amma ya nuna halin ko-in-kula, lamarin da ya haifar da wannan babban rashin,” in ji SP Adeh.

‎Rundunar ta ce bayan faruwar lamarin, an yi gaggawar ceto yaron tare da garzaya da shi zuwa asibiti, sai dai likitoci sun tabbatar da mutuwarsa sakamakon raunin da ya samu.

‎Da yake nuna alhininsa kan wannan lamari, Kwamishinan ’Yan Sanda na FCT, CP Benneth Igweh, ya bukaci iyaye da masu gidaje da su zamo masu lura da lafiyar muhalli da kuma kare rayuwar yara, yana mai cewa kulawar iyaye da gudanar da nagartaccen tsari a gidaje na da matuƙar muhimmanci wajen kare rayuka.

Advertisement

‎Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa an tsare wanda ake zargi yayin da bincike ke ci gaba domin ɗaukar matakin shari’a da ya dace.

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending