News
Rashin Gaskiya A Ka Ragal Mulki: EFCC Na Binciken Gwamnoni 18 Masu Ci — Olukoyede
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce hukumar na binciken wasu gwamnoni 18 da ke kan mulki a halin yanzu.
Ya bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai da aka gudanar a Legas, wanda ya hada masu shirya fina-finai da ‘yan canjin kudi domin tattauna matsalolin wulakanta takardun Naira da kuma lalata su.
Jami’an Tsaro Sun Cafke Mutum Bisa Mutuwar Yaro Ɗan Shekara Uku A Ramin Kwatar Gidansa
Da yake amsa tambaya daga mahalarta taron, Olukoyede ya ce hukumar ba ta jiran sai shugabanni sun gama mulki kafin ta bincike su.
“A lokacin da nake magana da ku yanzu, muna binciken gwamnoni 18 da ke kan mulki. Muna fara bincike tun suna ofis, kuma idan sun sauka sai mu shiga mataki na gaba,” in ji shi.
Shugaban EFCC ya ce wannan lamari na almubazzaranci da rashin gaskiya daga wasu shugabanni keyi hukumar za ta ci gaba da aikinta ba tare da la’akari da matsayin mutum ba.
