Connect with us

News

INEC: An Karɓi Buƙatar Rijistar Sabbin Jam’iyyu 144 A Fadin Ƙasa

Published

on

INEC Yakubu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa ta karɓi buƙatu har 144 daga ƙungiyoyin da ke neman samun rijista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya.

Kwamishinan hukumar kuma Shugaban Kwamitin Wayar da Kai da Ilimantar da Masu Zaɓe, Mr. Sam Olumekun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar daga birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.

Advertisement

Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Fiye Da Mutum 2,800 A Cikin Watanni 6 – FRSC

Ya ce, a cikin makonni baya-bayan nan ne hukumar ta karɓi ƙarin buƙatu guda 10, wanda hakan ya ɗora yawan ƙungiyoyin da ke neman zama jam’iyyun siyasa zuwa 144.

“Yanzu haka mun shiga matakin nazarin takardun buƙatu da kuma cikakken bincike kan ƙungiyoyin da suka gabatar da sha’awar zama jam’iyya, domin tantance waɗanda suka cika ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada,” in ji Olumekun.

Advertisement

Haka kuma, Olumekun ya bayyana cewa, a ƙarƙashin tsarin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR) da hukumar ke gudanarwa, mutum 168,187 ne suka yi rijista a jihar Anambra kacal.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending