Connect with us

News

ASUU Za Ta Tsunduma Yajin Aiki

Published

on

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU, ta sanar da shirin fara gudanar da zanga-zanga a jami’o’in gwamnati dake faɗin ƙasar, tare da barazanar tsunduma yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta gaza biya musu buƙatunsu.

ASUU, ƙungiya mafi girma a fannin ilimin Najeriya, ta sanar da shirin nata ne a wata takarda da shugabanta Christopher Piwuna ya fitar a ranar Alhamis bayan kammala taronsu a Sokoto.

Advertisement

Akwai Bukatar Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Najeriya Kamar Yadda Aka Yi A Lokacin Korona Domin Magance Matsalar Tsaro – Buratai

Ƙungiyar ta sanya ranar 28 ga watan Agusta a matsayin wa’adin da ta baiwa gwamnatin Najeriya domin ta yi duba kan buƙatunta, ko ta ɗauki mataki na gaba.

Cikin buƙatun da ASUU ta ke neman gwamnatin ƙasar ta biya ta har da na biya mata buƙatunta dake ƙunshe cikin daftarin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ƙungiyar a shekarar 2009, tare da sabunta ta.

Advertisement

Ƙungiyar ta ce ta bi hanyoyi da dama don ganin an cimma matsaya tsakaninta da gwamnati, ciki har da rubuta wasiƙu, baya ga jan hankalin gwamnati kan lamarin, amma har kawo yanzu ta gaza wajen magance su.

A don haka tayi kira ga mambobinta da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata domin gudanar da gangamin adawa da rashin cika musu muradansu a mako mai zuwa.

Advertisement

A shekarar 2022 ne ASUU ta shafe watanni takwas tana yajin aiki saboda rashin biyan haƙƙoƙinta, lamarin da ya jefa fannin ilimin Najeriya cikin mummunan yanayi.

 

Advertisement

 

FRI HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending