News
Amaechi Ya Caccaki Shugaba Tinubu Kan Yunwar Da Ta Addabi Ƴan Najeriya
Tsohon Ministan Sufuri na Najeriya Mista Rotimi Amaechi ya caccaki shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu kan halin yunwa da rashin tsaro da ƙasar ke ciki.
Rotimi Ameachi wanda ya kasance minista zamanin marigayi shugaba Muhammadu Buhari, ya ce mafi yawan yan ƙasar na fama da matsananciyar yunwa wadda har ta kai masu kuɗi ma ba komai suke iya ci ba yanzu saboda tsoron talauci.
Ɗan siyasar wanda tsohon gwamna ne na jihar Rivers, ya furta waɗannan kalamai ne a jihar Kano da yammacin ranar Laraba yayin wata ziyara da ya kai wa ƴan kasuwa a birnin da ke arewacin ƙasar.
Ya ce akwai bukatar gwamnati mai ci ta sake tunani game da harkokin kasuwanci da tattalin arzikin ƙasa, kasancewar ƴan kasuwa na fuskantar matsaloli masu sarƙaƙiya.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta kasa taɓuka komai kan matsalar tsaro, wadda ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar.
Dangane da batun tsayuwarsa takarar shugabancin ƙasar, Rotimi Ameachi ya ce lokaci bai yi ba, amma tabbas zai tsaya takakar domin kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
