News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Dakatar da Yin Amfani da ‘Yan Sanda Don Tsaron Manyan Mutane – Hadiza Bala Usman
Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta kawo ƙarshen amfani da jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen yi wa manyan mutane rakiya, tana mai jaddada cewa ba za a ci gaba da sadaukar da tsaron ƙasa don kare VIPs ba.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Hada-hadar Ayyuka kuma Shugabar Cibiyar Kula da Tsare-tsaren Ci gaban Ƙasa (CDCU), Hajiya Hadiza Bala Usman, ce ta bayyana haka a Abuja yayin taron nazarin ayyukan ma’aikatar cikin gida da aka gudanar a ranar Alhamis.
‘Yan Nijeriya Sun Biya Naira Biliyan 2.57 A Matsayin Kuɗin Fansa A Shekara Ɗaya – Rahoto
Ta nuna damuwa kan yadda ake karkatar da jami’an ‘yan sanda daga manyan ayyukan tsaron jama’a zuwa hidimar rakiya ga ‘yan siyasa da attajirai.
Hadiza ta ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiki kan gyara dokar Private Guard Companies Act domin bai wa kamfanonin tsaro masu lasisi damar ɗaukar nauyin tsaron VIPs, yayin da jami’an ‘yan sanda za su mayar da hankali kan aikin tsaron al’umma gaba ɗaya.
“Wanda yake ganin ya fi muhimmanci ya ɗauki jami’an tsaro masu bindigogi, zai biya kuɗin hayar kamfanin tsaro, ba wai a ci gaba da karkatar da jami’an ‘yan sanda daga aikin kare jama’a ba,” in ji ta.
Ta ce wannan mataki yana daga cikin muhimman manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu da aka sanya a cikin tsare-tsaren CDCU, tare da umartar ma’aikatar cikin gida da ta kammala gyare-gyaren dokokin kafin ƙarshen zangon uku na shekarar 2025.
