Connect with us

News

Faifen Bidiyon Dala: Tsohon Kakakin Ganduje, Ya Janye Shaidarsa Kan Ja’afar Ja’afar

Published

on

Wani sabon salo ya bayyana a rikicin siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bayan rahotanni sun ce tsohon Kakakin Yada Labaransa, Malam Abba Anwar, ya janye shaidar da ya bayar a kan ɗan jaridar nan Ja’afar Ja’afar, wanda shi ne ya wallafa shahararren Faifen Bidiyon Dala.

Bincikenmu ya nuna cewa tsohon Sakataren Yada Labarai na Ganduje, Abba Anwar, ya janye bayaninsa akan Ja’afar. Anwar ya kasance CPS na Ganduje tsawon shekaru 6, daga 2018 zuwa 2023, kuma yana daga cikin mafi kusa da shi.

Advertisement

Kotu Ta Yanke Wa Malamin Islamiyya Daurin Shekara 21 A Gidan Gyaran Hali A Kano 

Dalilin da ya sa Anwar ya dauki wannan mataki bai bayyana ba har zuwa lokacin da aka kammala rahoton.

An gabatar da bayanan Shaidar a shekarar 2022 a Ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hedikwatar Rundunar, Abuja.

Advertisement

Wannan sabon ci gaba na iya sa bidiyon dala da ke da nasaba da Ganduje ya sake daukar hankalin kotuna da masu shari’a.

A lokacin da aka fara wallafa bidiyon dala, ana zargin shaidun sun ce Ja’afar na kokarin bata sunan Gwamna Ganduje.

Advertisement

Sai dai janyewar wannan bayani na baya-bayan nan ya haifar da zazzafar muhawara da tambayoyi masu nauyi akan dalilan da suka sa aka janye bayanin.

Wata majiya kusa da lamarin, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana cewa janyewar bayanin na da alaka da rikicin siyasa da ke kara kamari a Kano, musamman dangane da gazawar tsohon gwamnan wajen hada kan jam’iyyar APC a matsayin day.

Advertisement

Yayin da Ganduje ke fuskantar suka daga tsofaffin abokan siyasa da kuma daga cikin jam’iyyar a matakin kasa, har yanzu ba a san yadda wannan ci gaba zai shafi matsayinsa a jam’iyyar da kuma aikinsa na siyasa gaba daya ba.

“Duk ƙoƙarin da aka yi na jin ta bakin Abba Anwar ya ci tura, duk da cewa a wata tattaunawa ta baya ya tabbatar da gaskiyar janyewar shaidar tare da ba da izinin wallafawa.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending