Connect with us

News

Ambaliyar Ruwan Sama Ta Ɗaiɗaita Yara 470, Ta Lalata Gidaje 270 A Zariya

Published

on

Jigawa Ambaliyar Ruwa Tayu Sanadiyar Mutuwar Mutane 16 Tare Lalata Gidaje 3,936 

Wani mamakon ruwan sama da aka tafka tsakanin Alhamis da Juma’a a Zariya, Jihar Kaduna, ya yi sanadin ɗaiɗaita yara sama da 470 tare da lalata gidaje akalla 270.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Zariya, Ahmad Muhammad Jaga, ya jagoranci tawagar haɗin gwiwa da ta ƙunshi jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Ƙungiyar Red Cross, domin duba yankunan da ambaliyar ta rutsa da su.

Advertisement

Jami’an Ƴan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Ƙaninsa Ya Ɓoye Gawar A Cikin Duro

Unguwannin da suka fi fuskantar barna sun haɗa da Ƙofar Kuyanbana, Gangaren Mobil, Bayan Cinema a Tudun Wada, Magume, Bako Zuntu da Kamacha a Tukur Tukur.

Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar ta shafe gidaje, ta lalata kayan abinci, da na’urorin lantarki. Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce sun shiga halin firgici lokacin da ruwan ya mamaye gidajensu, abin da ya tilasta musu ficewa a tsakiyar dare.

Advertisement

Tuni jami’an Red Cross reshen Zariya suka fara raba kayayyakin tallafi ga waɗanda abin ya shafa. Tallafin ya haɗa da abinci, barguna da ɗaukin gaggawa ga iyalai da suka rasa matsuguni.

Sai dai a sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa har yanzu akwai buƙatar ƙarin agaji duba da yadda mutanen da abin ya shafa suka shiga mawuyacin hali.

Advertisement

 

 

Advertisement

THE WHISTLER NEWSPAPER

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending