Connect with us

News

Hilda Baci Ta Dafa Buhu 200 Na Shinkafa A Yunƙurin Kafa Sabon Tarihi

Published

on

1757771904440 eplwf 6d8848edef8b43138da01eb908b37b6a251a0f158c0156e92d9d969e6b72f4e6

Fitacciyar mai girki ta Nijeriya, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake jan hankalin duniya bayan ta dafa buhun shinkafa 200 a wani yunƙuri na kafa sabon tarihi a duniya.

An gudanar da wannan gagarumin girki ne a fili a birnin kasuwanci na Legas, inda Hilda ta shafe awa takwas tana dafawa. Wannan ya jawo daruruwan jama’a da suka taru domin kallon abin da ke faruwa tare da ɗaukar hotuna da bidiyo.

Advertisement

Ambaliyar Ruwan Sama Ta Ɗaiɗaita Yara 470, Ta Lalata Gidaje 270 A Zariya

A girkin, Hilda ta yi amfani da shinkafa mai nauyin kilo 4,000, katan 500 na tumatir, kilo 600 na albasa, da sauran kayan haɗi.

Hilda ta shahara a shekarar 2023, lokacin da ta shiga kundin Guinness World Records bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girki ba tare da tsayawa ba.

Advertisement

Sai dai, kamar yadda aka saba, dole ne Guinness World Records su gudanar da bincike da tantancewa kafin su tabbatar da cewa Hilda ta kafa sabon tarihi.

Dafa-dukar shinkafa, wanda aka fi sani da jollof rice, abinci ne da ake sha’awa a ƙasashen Yammacin Afirka. Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru da Gambiya duk suna da’awar cewa su ne suka fi kwarewa a dafawa.

Advertisement

A shekarar 2023, UNESCO ta amince da Senegal a matsayin inda wannan abinci ya samo asali, daga jama’ar Wolof.

 

Advertisement

 

TRT GLOBAL 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending