Connect with us

News

Aƙalla Jami’an Tsaro 53 Ne Suka Rasa Rayukansu Cikin Mako 2 

Published

on

Aƙalla jami’an tsaro 53 da suka ƙunshi sojoji, da ‘yansanda, da na kula da kadarorin gwamnati, da kwastam da kuma na shige da fice ne aka kashe cikin makonni biyu a Najeriya.

Sauran jami’an tsaron da aka kashe cikin makonni biyu a Najeriyar sun haɗa da ‘yan sa kai, da na rundunar haɗin gwiwa ta JTF, da kuma ‘yan kwamiti na jihohi.

Advertisement

Samar Da Yan Sandan Jiha, Hanyar Haddasa A Fitina Ce – Tsohon AIG

Kodayake adadin jami’an da aka kashe bai ƙunshi waɗanda ba’a bayyana a hukumance ba.

Mafi yawan jami’an tsaron da lamarin ya rutsa dasu sun mutu ne a lokacin da ‘yanbindiga suka kai hare-hare a yankuna da dama a sassan ƙasar, yayin da wasu mutuwar ta riske su a shingayen bincike na tsaro.

Advertisement

Binciken da jaridar Daily trust ta gudanar a watan Disambar da ya gabata, ya gano yadda aƙalla jami’an ‘yansandan Najeriya 229 ne aka kashe tsakanin Janairun 2023 zuwa Oktoban 2024.

Hari na baya-bayan nan da ya afku shi ne a jihohin Benue da Kogi, inda aka kashe ‘yansanda da wasu jami’an tsaro 7 a hare-hare mabanbanta da ‘yanbindiga suka ƙaddamar a ranakun Juma’a da Asabar ɗin da suka gabata, yayin da aka yi garkuwa da jami’an tsaro da dama a harin na Benue.

Advertisement

Haka zalika, ‘yanbindiga da ‘yanta’adda da kuma mayaƙan Boko Haram, baya ga ‘yan fashi da makami, da kuma ƙungiyoyin asiri ne keda alhakin kisan jami’an tsaron.

To sai dai hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta samu nasarar gurfanar da mutane 9 gaban babbar kotun tarayya dake Abuja, kan zarginsu da hannu a hare-haren baya-bayan nan da aka kai a jihohin Benue da Filato.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending