News
Cutar Mashaƙo Ta Yi Ajalin Mutum Biyu A Kaduna
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa an rufe wasu makarantun gwamnati bayan ɓullar cutar mashaƙo wato diptheria a jihar, inda ta ti sanadiyar kashe mutum biyu.
Kwashishinar lafiya a jihar, Hajiya Umma K. Ahmed ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce sun killace wasu da dama a sanadiyar ɓullar cutar, amma sun samu sauƙi, kuma an sallame su.
Jami’in ‘Yan Sanda Da Wata Mata Sun Rasa Rayukansu Bayan Kwantena Ta Murkushe Adaidita Sahu
Cutar mashaƙo dai cuta ce da take shaƙe mutane, sannan ta sarƙe musu numfashi, lamarin da ke kai wa ga kashe mutum idan ba a kai masa matakin gaggawa ba kamar yanda BBC HAUSA ta ruwaito
Advertisements
