News
An Sace Motar Ƴansanda A Harabar Hedikwatar Rundunar A Abuja
Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da cewa wasu bata-garin sun sace wata motar aiki mallakar rundunar a cikin harabar hedikwatarta, Louis Edet House, da ke babban birnin tarayya Abuja.
A cewar rahoton da Sashen Binciken Manyan Laifuka (FCID) ya fitar ta hannun kwamishinan ƴansanda na DFA ofishin Katsina, motar da aka sace ita ce ƙirar Toyota Buffalo Land Cruiser mai lambar rijista NPF 5594 D da chasis mai lamba JTELU71JX0B027126. An ruwaito cewa ta ɓace ne tun ranar 28 ga Yuli, 2025 daga wurin ajiye motocin hedikwatar.
Jihar Borno Ce Ta Fi Kowace Jaha Yawan Masu Rajistar Katin Zaɓe Ta Yanar Gizo – INEC
Motar, wadda ke ƙarƙashin Sashen Ayyuka (Department of Operations) na rundunar, an gano ɓacewarta ne bayan an lura cewa ta ɓace daga inda aka ajiye ta ba tare da wani izini ba.
A cikin wata sanarwa da rundunar ƴansanda ta fitar, ta bayyana cewa:
“An sanar da jama’a cewa motar runduna mai lambar rijista NPF 5594 D, da aka ɗora wa Sashen Ayyuka na Hedikwatar Abuja, ta ɓace ko kuma an cire ta daga wurin ajiye motocin ranar 28/07/2025. Ana ci gaba da gudanar da bincike. Dukkan kwamandoji, DPOs da sauran rukunan rundunar a fadin ƙasa su sanya ido domin gano motar.”
Rundunar ta kuma bukaci dukkan jami’an tsaro a fadin ƙasar da su ɗauki lamarin da matuƙar muhimmanci tare da ba da rahoto cikin gaggawa idan sun samu wani bayani da zai taimaka wajen gano motar da aka sace.
