News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Karbar Haraji Daga Hannun Mata Masu Zaman Kansu.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara cire haraji daga kuɗaɗen da mata masu zaman kansu, musamman masu karuwanci, ke samu a ƙarƙashin sabon tsarin haraji da ake shirin aiwatarwa a ƙasar.
Taiwo Oyedele, shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, ne ya bayyana hakan a wani bidiyo da aka wallafa a shafin X a ranar Litinin, inda ya yi karin bayani kan hanyoyin samun kuɗi da dokokin haraji ke ɗauka.
An Sace Motar Ƴansanda A Harabar Hedikwatar Rundunar A Abuja
Oyedele ya bayyana cewa sabon tsarin haraji ba ya bambance tsakanin hanyar halal ko haram wajen samun kuɗi, domin abin da ake dubawa kawai shi ne ko kuɗin ya fito daga wani aiki ko sayar da kaya.
“Ga wani misali idan mutum ko mace suna yin dadiro, suna neman maza su kwanta da su, wannan aiki ne, kuma za a ɗauki haraji a kai,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dokar haraji ba ta tambayi ko aikin halal ne ko a’a. “Abin da take tambaya shi ne, shin kana samun kuɗi? Shin ka samu kuɗin ne ta hanyar aikin da ka yi ko sayar da kaya? Idan haka ne, to sai ka biya haraji.”
Sai dai Oyedele ya bayyana cewa kyaututtuka ko kuɗin taimako da ake aikawa ‘yan uwa, abokai ko baƙi ba sa cikin abin da za a ciro haraji akai, domin ana ɗaukar su a matsayin kyauta ba musayar aiki ba.
Wannan matakin na cikin sabon tsarin gyaran haraji da gwamnati ke ƙoƙarin aiwatarwa domin ƙara yawan kudaden shiga da kuma faɗaɗa hanyoyin samun haraji a ƙasar.
