News
Ku Gaggauta Sakin Zakariyya Gwagwarwa Ba Tare Da Wani Sharadi Ba —CITAD
Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta sakin ɗan bautar ƙasa, Zakariyya Kabeer Gwagwarwa, wanda ƴan sanda a Jihar Katsina ke tsare da shi bisa abin da cibiyar ta bayyana a matsayin kama da tsarewa ba bisa ƙa’ida ba.
A wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na CITAD, Malam Y.Z. Ya’u, ya fitar a ranar Talata, cibiyar ta bayyana cewa kama Zakariyya da tsare shi saboda wani rubutu da ya wallafa a shafin Facebook babban take ne ga kundin tsarin mulki da ya bai wa ’yan ƙasa ’yancin faɗar albarkacin baki.
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Karbar Haraji Daga Hannun Mata Masu Zaman Kansu.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Zakariyya ne bayan umarnin wani ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Nassarawa a Jihar Kano, saboda rubutun da ya wallafa yana cewa:
“Company Pampers must go Sabuwar Nassarawa 2027 Insha Allahu.”
CITAD ta ce wannan rubutu ba ya ɗauke da kalaman da za su iya tayar da rikici ko barazana ga zaman lafiya, sai dai yana nuna ra’ayinsa ne kan harkar siyasa – abin da doka ta ba shi dama
Sanarwar ta bayyana cewa an tsare Zakariyya har tsawon kwanaki ba tare da damar tuntuɓar iyayensa ko lauya ba, sannan daga baya aka gurfanar da shi a kotu.
Duk da haka, maimakon a ba shi belin wucin gadi, kotun ta dage shari’ar har na mako biyu, abin da CITAD ta kira karya haƙƙinsa.
Haka kuma, cibiyar ta ce ta samu rahotannin cewa an ci zarafinsa da duka a lokacin da yake tsare, lamarin da ta bayyana da cewa ya sabawa doka kuma abin ƙyama ne da ya kamata a bincika, sannan a hukunta waɗanda suka aikata hakan.
“Ƴan sanda dole su kare kundin tsarin mulki. Ƙuntata wa ’yan ƙasa saboda ra’ayinsu hanya ce ta jefa ƙasa cikin mulkin kama-karya,” in ji Y.Z. Ya’u.
