Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Ɗan Kasuwa Da Ya Ɓoye Koka’in A  Gabansa A Filin Jirgin Saman Kano

Published

on

IMG 20251012 114854

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wani ɗan kasuwa mai shekara 52, mai suna Ejiofor Emeka, a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano International Airport (MAKIA) bisa zargin ƙoƙarin shigar da koka’in da ya ɓoye a gabansa.

A cewar hukumar, Emeka wanda ke da shagunan kaya a Legas da Onitsha a Jihar Anambra, an kama shi ne bayan isowarsa daga Bangkok da kuma ƙasar Thailand, ta jirgin Ethiopian Airlines ET 941 a ranar Laraba, 8 ga Oktoba, 2025, sakamakon samun sahihin bayanan sirri daga jami’an tsaro.

Advertisement

KATSINA:Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana cewa binciken body scan ya nuna cewa wanda ake zargin ya haɗiye wasu ƙwayoyi tare da ɓoye wasu a cikin sassan jikinsa.

“An samo wraps 58 na koka’in daga wandon sa nan take, sannan aka kai shi wurin lura inda ya fitar da pellets 69 a cikin bayan gida a lokuta bakwai, wanda gaba ɗaya suka kai wraps 127 da nauyin kilogiram 1.388,” in ji Babafemi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending