Connect with us

News

‎Wata Matar Aure Ta Fasawa Mijinta Ido Da Wuƙa A Neja

Published

on

1758622702522

Wata mata mai suna Halima Salisu ta shiga hannun ’yan sanda a jihar Neja bayan da ta kai hari ga mijinta, Salisu Suleiman, inda ta yanka masa wuya tare da fasa masa ido da wuƙar girki.

‎Lamarin ya faru ne a garin Kuta, hedikwatar karamar hukumar Shiroro, da safiyar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na asuba, kamar yadda rundunar ’yan sanda ta tabbatar.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 19 Don Ayyukan Ci Gaban Al’umma

‎Majiyoyi sun shaida cewa ma’auratan sun samu saɓani ne kafin lamarin, inda matar ta jira mijinta ya kwanta barci, sannan ta ɗauki wuƙar girki ta kai masa hari.

‎Wani mazaunin garin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “An wayi gari da hayaniyar mutane suna ihu. Matar ta riga ta soka masa wuƙa a wuya da kuma ido, kafin a garzaya da shi asibiti.”

Advertisement

‎Kakakin ’yan sanda na jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai wanda abin ya faru da shi asibitin gabaɗaya na Kuta, kafin daga bisani a asibitin ƙwararru na IBB da ke Minna domin ƙarin kulawa.

‎“An kama matar da ake zargi kuma tana tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike, kafin a gurfanar da ita a gaban kotu,” in ji Abiodun cikin sanarwar da ya fitar.

Advertisement

‎Har yanzu ba a san ainihin abin da ya haifar da sabanin tsakanin ma’auratan ba, sai dai hukumomi sun ce bincike na ci gaba da gudana.

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending