Connect with us

News

Kotu Ta Yanke Wa Manajar Banki Hukuncin Daurin Shekara 5 A Gidan Yari A Adamawa 

Published

on

Screenshot 2025 10 31 033816

Wata kotun jihar Adamawa karkashin mai shari’a Benjamin Lawan Manji ta yanke wa Grace Karka, manajar Bonghe Micro Finance Bank, hukuncin daurin shekara biyar a gidan gyaran hali bayan ta sami laifi kan zargin almundahana da hukumar EFCC ta gabatar.

A cewar sanarwar EFCC, Karka ta fuskanci tuhuma guda biyu da suka shafi haɗin baki da zamba, inda ake zargin ta da karkatar da sama da naira miliyan 32 daga asusun bankin da take jagoranta.

Advertisement

‎Wata Matar Aure Ta Fasawa Mijinta Ido Da Wuƙa A Neja

A cikin shari’ar da aka gabatar, EFCC ta bayyana cewa Grace Karka da abokinta Prince Moses Batalu sun yi amfani da damar mukaminta wajen cire kudaden bankin ba tare da izini ba daga asusun da ke First Bank Nigeria Limited.

Da aka fara sauraron karar a ranar 11 ga Nuwamba, 2024, Karka ta musanta laifin, amma kotu ta ce bayan shaidun da aka gabatar, an tabbatar da laifin nata ba tare da shakka ba.

Advertisement

Mai shari’a Manji ya bayyana hukunci a ranar 17 ga Oktoba, 2025, inda ya yanke mata hukuncin shekara biyar a kurkuku tare da zabin biyan naira miliyan uku (₦3m) a kowace daga cikin tuhume-tuhumen guda biyu, kuma hukuncin zai gudana lokaci guda.

Kotun ta kuma umarci ta dawo da kudaden da suka rage, kimanin ₦29.8 miliyan, ga bankin da ya shigar da kara.

Advertisement

Rahoton EFCC ya ce an gano barnar ne bayan bankin ya gudanar da binciken kudi a 2021, inda aka gano cewa Karka ce da kanta ta tura kudaden zuwa wani asusun mutum da ba abokin hulɗar bankin ba ne, kuma duk ƙoƙarin dawo da kuɗin ya ci tura.

 

Advertisement

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending