News
Himma Radio 91.1FM Ta Dauki Nauyin Sanya Yara A Makaranta A Kano
Gidan rediyon Himma 91.1FM da ke Kano ya kaddamar da wani shiri na tallafawa ilimi, inda ya dauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a yankin Kafin Agur, karamar hukumar Madobi, a jihar Kano.
An gudanar da bikin kaddamarwar a harabar gidan rediyon a ranar Lahadi, 2 ga Nuwamba 2025, inda manyan baki daga sassa daban-daban na jihar suka halarta.
Kotu Ta Yanke Wa Manajar Banki Hukuncin Daurin Shekara 5 A Gidan Yari A Adamawa
A yayin taron, an bai wa yara maza da mata cikakkun kayan makaranta — ciki har da uniform, jakunkuna, litattafai da kayan rubutu, domin su fara sabuwar rayuwa ta neman ilimi.
Cikin manyan bakin da suka halarci taron akwai Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano, Alhaji Sale Musa Sale, Wakilin Gwamnan Kano, Alhaji Sale Musa Wailari, Wakilin Shugaban Karamar Hukumar Madobi, Hon. Nasir Sulaiman, da kuma Dr. Balabe Danlami Jazuli, wanda ya wakilci Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB).
Haka kuma, Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Haruna Musa, ya halarci bikin a matsayin bako na musamman.
Da yake jawabi, Shugaban Himma Radio, Alhaji Ismail Yusuf Makwarari, ya ce manufar shirin ita ce tallafa wa al’umma ta hanyar tabbatar da cewa yara daga gidaje masu karamin karfi sun samu damar zuwa makaranta.
“Mun dauki wannan mataki ne domin taimaka wa wadannan yara da iyayensu. Mun fahimci cewa noma na zamani ba zai yiwu ba sai da ilimi. Kuma tunda yawancin shirye-shiryenmu na da alaka da noma, mun ga dacewar mu tallafa wajen sanya yara a makaranta domin su zama manoma masu ilimi a nan gaba,” in ji Makwarari.
Ya ce Himma Radio za ta ci gaba da fadada irin wannan shiri zuwa sauran kananan hukumomi na jihar Kano domin tabbatar da cewa ilimi ya karade ko’ina cikin jihar.
A nasa bangaren, Wakilin Gwamnan Kano, Alhaji Sale Musa Wailari, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa ya yi daidai da manufar gwamnatin Kano ta inganta harkar ilimi da rage jahilci a tsakanin yara.
“Gwamnatin Kano za ta yi hadin gwiwa da Himma Radio wajen fadada irin wannan shiri a fadin jihar domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar zuwa makaranta,” in ji shi.
Shi ma Hakimin Madobi, Alhaji Sale Musa Sale, ya bayyana farin cikinsa da yadda aka gudanar da shirin a gundumarsa, inda ya yaba da jajircewar Himma Radio wajen bunkasa ilimi, tare da yin alkawarin bayar da goyon bayan da ya dace.
Daya daga cikin iyayen yaran da aka sanya a makaranta, Sani Ismail, ya nuna farin cikinsa da godiya bisa wannan taimako.
“Mun daɗe muna son mu tura ’ya’yanmu makaranta, amma rashin hali ya hana. Yanzu wannan taimako daga Himma Radio zai taimaka musu su yi gaba a rayuwa,” in ji shi cikin murna.
Taron ya gudana cikin nishadi da girmamawa, yayin da Himma Radio 91.1FM ta tabbatar da jajircewarta wajen inganta ilimi da raya al’umma, musamman a fannonin noma da wayar da kan matasa.
